​A SHORT HISTORY OF GARUNGABAS. BY K. L. HALL…. 


Garungabas generally recognised as the ancient Biram, i believe and Bagdaza to be Baghdad. The legend in another form is connected with that of the Origin of the Hausa Bakwai. Mukhtar or Bayajidda was compelled to flee Bornu with his wife, on his Journey west he left her on the road and she gave birth to Biram who founded Garungabas. Bayajidda continued his journey to Daura where the well known encounter with the Snake took place and Bayajidda’s marriage with the Queen Daurama. 
The Town was founded by Arabs from Baghdad, one Mukhtar and his younger brother Biram migrated West and came to Birnin Bornu (Kukawa). The Shehu of Kukawa gave Mukhtar his daughter in marriage and the town of Kulunfardu where he lived until his death. Biram and his younger brother then migrated further West and founded Garungabas. 
The following is a list of Chiefs of Garungabas. 

1. BIRAM 

2.BOMI… One of the Biram’s follower who came with him from Kulunfardu but no relation. 

3. TUNKU… Also one of the Biram’s followers. The length of time for which these three held the Sarauta unknown. 

4. ABDULLAHI. Called Ajab… He ruled for three days and then miraculously disappeared. 

5. ASAWA… Thirty years the grandfather of the present Sarkin Gabas, he was deposed by Sambo Diginsa the first Fulani Emir of Hadejia, on account of his son was murdered. 

6. MUSA… Nephew of Asawa Eleven years, appointed by Sambo. 

7. GAUYAMA… Not of the ruling family fourty years, half way through his reign he became blind. 

8. BARWAI… Younger brother of Sambo, Nine years. 

9. USMAN… Son of Barwai, Six years he then Emigrated to Shira. 

10. GABDO…  One year and Emigrated to Katagum. 

11. BURMI…  A fulani,  one year fled to Katagum in terror of Buhari. 

12. SARKIYO…  One of the Buhari’s “Hakimi” Ten years, Buhari then died and was succeeded by Umaru who remove Sarkiyo to Hadejia and made him Barwa.

13. MUHAMMAD BAKO… Son of Asawa and thus descendent to the Original Arab founders, Appointed by Haru Bubba. He held the Sarauta for Two years and then went to Mecca. 

MUHAMMAD DARINGI… A fulani,  seven month deposed by the Emir. 

15. TUKUR… Son of Gauyama, after five years of his rule Muhammad Bako returned from Mecca,  but leave as a private individual. Muhammad Tukur ruled for another five years and was then deposed by Haru for shaving his wife’s head. 16. KANKARAU… A fulani appointed by Haru, but deposed after seven month.  Muhammad Tukur Was then reinstalled and rule for seven years when he became blind and was deposed. KANKARAU reinstated but after seven years was again deposed by the Emir Muhammadu for having married seven wives. 

      The Emir then called in all the man of Garungabas to choose their own Chief. They unanimously choose Abubakar son of Muhammad Bako a direct descendant of the original Arab founders. Abubakar at first however persistently refused to accept the honour and on being pressed for a reason, told the Emir that as an Arab who had been to Mecca he could not countenance the perversion of the prophet’s laws which was rife in Hadejia.  The Emir is then stated to have admitted the Truth of this and on condition that he would take the Sarauta to have promised that he should administer according to the true Law at any rate in Garungabas. 
Abubakar then became Chief and has been Sarkin Gabas for twenty three years to the present day. The famine in common with other Hadejia District, the famine last year was the cause of considerable mortality chiefly among the children. 

Reference— Assessment reports by K. L. Hall, Assistant District officer Hadejia District Kano Province. 

​Daga Mallam Muhammad Rabakaya… 


A madadin al’ummar Hadejia da gaba dayan masarautar Hadejia muna addu’a da alhinin Marigayi Alhaji Adamu Kwano (kwano baka karaya) Allah ka gafartawa wannan bawa naka, ka yafe masa kura kurensa da iyayenmu Allah ta’ala kasa aljannah madaukakiya ce makomarsu. Alhaji Adamu Kwano miliyoyin mutane sunyi tarayya da ‘ya’yansa wajen gadon dukiyar da Allah ya mallaka masa Allah ka hada mu a Aljannah. zaka\ki so ka\kiji dalili -biyoni………………
Duk wadda ya baka Ilmi ko yayi ma hanyar samun Ilmi ya gama maka alfarma kuma kaci gado daga cikin gadonsa tare da ‘ya’yansa.    Marigayi Alhaji Adamu Kwano Hadejia Tun kafin a haifeni wannan bawan Allah yana da gida babba mai kallon gidanmu (Gida na a yanzu) Rahama chemist a yanzu ya gina yayi fasalin ajujuwa na Kasa da rufin kwano ya maidashi makarantar  Islamiyya (islamiyyar farko a garin Hadejia), ya tafi kano ya samo Marigayi Malam Aminu Yusuf da Malam Alhaji da Malam Sabo na Madabo da Malam Nasiru Ahli da Malam Rufa’i Kafin Hausa  kuma a matsayin Headmaster da malamai, kuma yabasu mahalli a wancan lokacin mun samu tabbaci daga matar daya daga cikinsu cewa daga gidansa ake dauko musu abinci. Aka saka yara maza da mata aka fara koyarda su darussan addini a tsarin zamani (formal education) mai Allo da Alli.

Daga nan abu ya kara fadada, yasa kudinsa ya cike wani rami mai tarihi wato RAMIN MALAM HUDU inda ya gina ajujuwa na siminti akan ramin da staffroom islamiyya ta koma can ya kara malamai, lokacin duk babu islamiyya sai ita Hudu islamiyya prim. sch. mai tsohon tarihi daga nan gwabnati ta shigo ta taimaka masa da karin Malamai da tsare tsare, Amma gini da gudanarwa nasane.

Bai tsaya nan ba tashinsa zuwa Asibiti inda yake aiki, ya sayi fili anan farin gida ta yanzu ya kara Gina wasu ajujuwan islamiyya ya bude makarantar Islamiyya Garko, duk a lokacin babu Islamiyya sai dai makarantun mu na zaure da na allo, daga nan ya kara fadada niyyarsa da burinsa na habaka ilmin addini a Hadejia ya raba Islamiyya Garko ya Kirkiri Karamar sakandare Islamiyya yasa mata sunan Headmaster na makarantarsa ta farko  wato Malam Aminu Yusuf. Ya sake samo wani mutumin Sudan Sheik Ali Fu’ad a matsayin principal inda ya dauka mata malamai itace Aminu Yusuf Junior Islamiyya sec. sch. Hadejia. Wadda daga baya gwabnati ta bashi wani bangare a cikin Buhari primary school Hadejia ta tashi daga Garko ta koma can inda takoma hannun gwamnati kachokam bayan Allah ya masa rasuwa, wannan makaranta yanzu itace babbar sakandaren Islamiyya ta jeka ka dawo ta mata da maza a garin Hadejia.
Daga wancan lokacin zuwa yanzu mutum nawa aka raya? mutum nawa su kuma nawa suka raya da Ilmi? Kuma Bayansa tayi kyau, yana da ‘ya’ya da jikoki da sukayi karatun Addini da Boko a fannoni da dama, da wadda yayi digirin farko tun 1977 har zuwa yau agida da kasar waje, sannan kafin yabar aiki yana daya daga cikin wadanda Gen. Olusegun Obasanjo ya baiwa lambar yabo yana shugaban Kasa  a shekarar 1977.
Da fatan zamuyi koyi da irinsu  a duk  bangarorin rayuwa.

DAGA MUHAMMAD IDRIS

image

FARFESA HARUNA WAKILI……………Farfesa Wakili haifaffen kofar fadar Hadejia ne, kuma kamar yadda sunansa ya nuna mahaifinsa shi ne Wakilin kudun Hadejia [Dandalma] wato mai kula da yankin kudancin garin Hadejia.

Farfesa Wakili shi ne Farfesa na biyu a masarautar Hadejia kuma yana daya daga cikin `yan majalissar dattijai na Jami`ar Bayero ta kano kuma babban Alaramma a tsangayar tarihi ta makarantar, harwayau shi ne Mufti akan harkar tarihi a Arewacin kasar nan dominkafafen watsa labarai da dama na ciki da wajen Nijeriya suna dogara da fatawowinsa wajen warware matsalolin tarihi da suka bujuro musu.Baya da harkokinsa na cikin Jami`a Farfesa Haruna Wakili ya rike Daraktan Cibiyar Nazarin Harkokin Siyasa na Jami`ar wato MUMBAIYA dake Gidan Malam Aminu Kano a Unguwar Gwammajar kano.

” Na zaune bai ga gari ba”, wanda bai sanJami`a ba, ba zai san gudunmawar Wakiliba domin a shekaru ashirin da biyar da suka gabata duk dan masarautar Hadejia da ya je Bayero ofishin Wakili ne zangonsa, shi kansa ba zai iya kididdige daliban da ya yi wa hanyar karatu a jami`a ba.

“Mai kamar zuwa kan aika” Yana cikin wannan gwagwarmaya Allah [swt] ya yi masa kwamishinan Ilmi na Jihar Jigawa. wannan mukami nasa duk Bahadeje mai hankali ba zai taba mantawa da shi ba domin baya da ci gaba a gyaran makarantu da samar da aiyuka da matasa da ya yi to kuma a lokacinsa babbar bukatarmu da muka dade muna nema ta neman babbar makaranta ta kai ga biya wato muka samu Jami`ar Kafin Hausa kuma aka gina babbar makarantaraiyukan gona ta Hadejia ta bar lungu ta dawo kan hanya.

Farfesa Haruna Wakili cikakken Bahadeje ne ba ya son raini amma yana da kishin al`ummarsa yana son ci gabansu kuma saboda daga darajar wannan masarauta shi rubutunsa ma na digirinsa na biyu akan wannan Masarauta ya yi.a takaice dai rayuwarsa akan bautawa Ilmi take.Hadejawa suna addu`a Allah Ya ba gwanin yafe gwado.

FARFESA HARUNA BIRNIWA…………kamar yadda sunansa ya nuna Farfesa Haruna Birniwa haifaffen garin Birniwa ne kuma yana cikin haular masu mulkin garin.Birniwa shi ne farfesa na farko a cikin wannan masarauta kuma farfesa nabiyu a fadin Jihar Jigawa.

Gaba daya rayuwar Birniwa a kan bautawa Ilmi take domin ya kasance daya daga cikin dattawan malamai a Jami`ar Danfodiyo dake Sokoto na shekaru masu yawa kuma ya rike ‘provost’ a kwalejin Ilmi dake Gumel sannan ya rike kwamishinan Ilmi a wannan Jiha.

Farfesa Birniwa ya bayarda gudunmawa a fagen bayarda ilmi a Jihar nan matuka domin daruruwan mutane sun ci moriyarzamansa a sokoto domin shi ‘admission’ a wurinsa kamar mutum ya mari budurwa ne don haka za a ya ce wa shi ne ya budewa Hadejawa kofa a sokoto kuma bai bar sokoto ba sai da ya yi dashe.

Lokacin yana ‘provost’ ma masu rabo sun samu aiki a wurin.Birniwa ba harkar ilmin zamani kadai ya tsaya ba domin fakihi ne a fannin addini kuma fahintarsa da addini ta kara sa kyawawan halayensa sun kara kyautata domin mutum ne mai hakuri da gaskiya da rikon amana da saukin kai.wani abun sha`awa ga halayensa mai unguwarsa a Hadejia ya ce in dai yana gari duk yadda za a je neman ci gaba da shi ake yi. munaaddu`a Allah ya albarkaci bayansa.

Posted from WordPress for Android via Hadejia A yau. http://Isabohadejia.blogspot.com

HADEJIAWA

DAGA Engr Idris Ali HADEJIAWA

image

View original post 253 more words

DAGA Engr Idris Ali HADEJIAWA

image

Read the rest of this entry »

TARIHIN HARUNA UJI DA WAKOKINSA. KASHI NA BIYU (2)..

Hadejia A yau!
image

Alh. Haruna Uji Hadejia.

Littafin Muhd. Aji Hadejia.
A kashi na farko kunji cewa Alh. Haruna Uji ya ci gaba da kidan Gurmi gadan gadan.

A lokacin Gwamnan Kano Abdu Bako, sai yaji labarin Haruna Uji, sai yasa aka nemoshi domin yayi masa waka akan wayar da kan Al’umma akan Noma. Saboda haka Gwamna Abdu Bako sai ya hadawa Haruna Uji kayan wasa, kamar Amsa Kuwwa (Loud speaker) da Abin Magana wato (Microphone) da Injin wuta, wato Generator.
Wannan shine lokaci na farko da Haruna Uji ya fara waka da kayan wasa na zamani, kuma ya kama yin waka gadan gadan a matsayin sana’a.

Wakar da yayi a lokacin Itace wakar Noma. Anyi wakar ne da nufin wayar da kan Talakawa su koma Aikin gona.

3.0. WAKOKIN HARUNA UJI NA FARKO.

Alh. Haruna Uji yayi wakoki masu tarin yawa, kuma a cikin Jerin wakokinsa ga wasu daga cikin wakokin da ya fara yi.

*Wakar Naira da kwabo sabon kudi.

*Wakar Gudaliya.

*Wakar Shamuwa.

*Wakar Noma.

*Wakar Bakar Rama.
Wadannan sune kusan Shahararrun wakokin da ya fara yi.

3.1. Ajin Haruna Uji a tsakanin Mawakan baka.

A cikin wani Littafi da Ibrahim Yaro Yahya da Abba Rufa’i suka tsara, Mamuda Aminu ya kawo rabe-raben Mawakan baka zuwa rukunai kamar haka:
*Mawakan Sarakuna
*Mawakan ‘yan mata
*Mawakan Jama’a
*Mawakan Mafarauta. Da sauransu.

Ya kawo misalin Mawakan Jama’a shine wanda zai yiwa Sarakuna da ‘yan kasuwa da ‘yan mata da Masu kudi da talakawa waka. Misali Mamman shata da Haruna Uji da sauransu.

Hakan ta nuna cewa Haruna Uji ya kasance a cikin Mawakan Jama’a, domin ya tabo duk abinda aka zayyana a sama. Wato yakan yiwa kowa waka.

3.1.1 Dangantakar Haruna Uji da Mawakan Baka.

Alh. Haruna Uji yana da kyakkyawar dangantaka da sauran ‘yan uwansa mawakan baka, yana girmamasu shima suna girmama shi, sannan ya hori wasu suma sun zama shahararrun mawaka a kasar Hausa. Yayiwa wasu waka kuma shima wasu sunyi masa. A cikin mawakan da suka masa waka har da Alh. Mamman shata, kuma shima Haruna Uji yayi wa Alh. Garba sufa wakar Ta’aziyya bayan ya mutu.

3.1.2 Jerin wasu daga wakokin Haruna Uji.

Bayan rukunin wakokinsa na farko, ga wasu daga cikin wakokin da yayi.

*Wakar Dankabo
*Wakar Alh. Sani Likori
*Wakar Direban Chiyaman
*Wakar (Air vice marshal) Ibrahim Alpha
*Wakar (kwamishinan ‘yan sanda) Daudu Gwalalo
*Wakar Haruna karamba
*Wakar Adamu Hassan Abunabo
*Wakar Ahmed Aruwa
*Wakar Asabe Madara
*Wakar Amadu koloji makwallah
*Wakar Bako Inusa kano
*Wakar Balaraba
*Wakar Jimmai Aljummah
*Wakar Birgediya Abdullahi shalin.
*Wakar Dankamasho
*Wakar Fulanin Jebbi fulato
*Wakar Idiyo Mai kayan Babur
*Wakar Kainuwa.

SAURAN WAKOKIN KU DUBA LITTAFIN.

Ka duba kashi na uku (3)

%d bloggers like this: